Posts

Showing posts from September, 2017

YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI!!! SHAWARWARI ASHIRIN (20)

Image
Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai babu abokin tarayya, Tsira da Aminci su tabbata akan wanda babu wani Annabi bayansa, da iyalan gidansa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa rana sakamako. Bayan haka; Wannan wata nasiha ce  da aka gabatar a wajen walimar wata daga cikin ‘yan uwa (Allah ya bata zaman lafiya). Kamar yadda yake, mata na kaunar ace sun mallake zukatan mazajen su, ta yanda kowane lokaci mazajen suna jin dadin zamantakewar su da matan kuma suna kaunar su matuka, ta yanda wannan yakan kai wasu matan zuwa ga halaka ta hanyar neman wannan (mallake mazajensu) inda wasu ke zuwa wajen bokaye da malaman tsibbu. To ‘yar uwa albishirin ki, zaki iya mallake mijin ki ta hanyar da addini ya yarda, wannan hanya itace kyautata mu’amala tsakanin ki da shi, kamar yadda wani mai hikima yake cewa acikin wasu baitoci; Ka kyautatawa mutane zaka mallake zuciyar su, saboda sau da yawa kyautatawa ta kan bautar da mutum (wajen wanda yake kyautata...