Posts

Showing posts from March, 2018

Labarin wadda Shan miyagun ƙwayoyi ya tarwatsa mata rayuwa.

Image
Wannan baiwar Allah da abin ya shafa, itace da kanta ta bada wannan labari nata mai cike da sosa zuciya da kuma ban takaici, kamar yadda Ash-Shaykh Muhammad Bn Abdirrahman Al-Arify (Daya daga cikin Malamai masu Da’awah a kasar Saudiyya) yake hakaito mana. Wannan baiwar Allah take cewa: “Mahaifi na *Limamin Masallaci* ne, a lokacin da na kammala karatun makarantar sakandire ni da Ɗan uwa na, sai mahaifin mu ya tura mu wani gari domin ci gaba da karatun mu na gaba da sakandire a can, a lokacin ina ‘yar shekara 17 shi kuma Ɗan uwa na shekarar sa 19. Bayan da muka isa garin da mahaifin mu ya tura mu karatu, sai muka kama hayar wani gida a cikin gari (mai dauke da dakuna sashe biyu -2 apartments-) ni da Ɗan uwa na, haka nan dai muka fara karatu muka shafe kusan shekara daya muna karatu, a kullum muna yin Magana da mahaifin mu ta wayar salula, duk lokacin hutu sai mu koma gida in ya kare mu dawo makaranta, muna kula da karatun mu sosai, muna kula da Ibada da kuma sallah akan lokaci...