Ko cutar Coronavirus (Covid-19) Na Iya Shiga Makkah Da Madinah?
Bayan hukumomin Saudiyya sun fitar da sanarwar dakatar da Umrah zuwa wani lokaci saboda Covid-19, cece-kuce ya kaure tsakanin mutane kan ko yana yiwuwa Covid-19 ta shiga Makkah da Madinah ko a'a? Masu ganin cewa cutar ba za ta iya shiga waɗannan garuruwa biyu masu alfarma ba na kafa hujja ne da hadisin da Bukhari (1880) da Muslim (1379) suka rawaito cewa Annabi (SAW) yace: (عَلَى أَنْقَابِ الْمَدِينَةِ مَلَائِكَةٌ لَا يَدْخُلُهَا الطَّاعُونُ وَلَا الدَّجَّالُ) (Akwai wasu mala'iku tsaye a ƙofofin Madinah, annoba da Dujal ba za su shige ta ba) Duba da wannan hadisi, mutum na iya cewa: annobar corona ba za ta iya shiga Makkah da Madinah ba. A wani hannu kuma, wasu daga cikin mallamai na ganin cewa annobar corona na iya shiga garuruwan, shi yasa ma mahukuntar ƙasa mai tsarki suka dakatar da yin Umrah don gudun kada wani daga wata ƙasa ya kai cutar harami. Waɗannan mallamai na ganin cewa wancan hadisi na sama, yana nufin wata annoba ce ƙayyadadda, ba duka a...