YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI!!! SHAWARWARI ASHIRIN (20)
Wannan wata nasiha ce da aka gabatar a wajen walimar wata daga cikin
‘yan uwa (Allah ya bata zaman lafiya).
Kamar yadda yake, mata na kaunar ace sun mallake
zukatan mazajen su, ta yanda kowane lokaci mazajen suna jin dadin zamantakewar
su da matan kuma suna kaunar su matuka, ta yanda wannan yakan kai wasu matan
zuwa ga halaka ta hanyar neman wannan (mallake mazajensu) inda wasu ke zuwa
wajen bokaye da malaman tsibbu. To ‘yar uwa albishirin ki, zaki iya mallake
mijin ki ta hanyar da addini ya yarda, wannan hanya itace kyautata mu’amala
tsakanin ki da shi, kamar yadda wani mai hikima yake cewa acikin wasu baitoci;
Ka kyautatawa mutane zaka mallake zuciyar su, saboda
sau da yawa kyautatawa ta kan bautar da mutum (wajen wanda yake kyautata masa).
Ga wadansu wasiyyoyi da shawarwari da idan ‘yar uwa
tayi aiki dasu zata mallake zuciyar mijin ta cikin ruwan sanyi, gasu kamar haka;
1. Ki yiwa mijin ki da’a kuma kada ki sabawa
umarnin sa, sai dai fa idan ya bukaci ki aikata abinda Allah (SWT) ya haramta,
saboda babu da’a ga abokin halitta wajen saba wa mahalicci, idan ya umarce ki
da sabon Allah, ki kame kada ki aikata, kuma kiyi amfani da hanyar da tafi
dacewa wajen yi masa nasiha da fahimtar dashi har ya canza ra’ayinsa akan wannan.
2. Ki yi mu’amala dashi da hanya mai kyau, da zance
mai dadi, sa’annan ki rika sanya yabo da jinjina da addu’a a cikin zancen ki,
kamar, Allah ya kara maka lafiya, Allah ya kiyaye min kai, da dai makamantan
su.
3. Ki rika yi masa kyaututtuka wani lokaci, komi
kan kantar ta, domin kyauta na kara aminci da kauna, kamar yadda Annabi SAW yace:
kuyi kyauta, zaku so junan ku.
4. Ki kasance koda yaushe cikin shiga mai kyau (ba
sai lokacin da zaki biki ba ko anguwa) kuma ki kula koda yaushe kada ya samu
abinda baya kauna daga wajen ki, saboda kulawar mace da tsaftar jikin ta da
kwalliyar ta yana daga cikin manyan sabubban da zasu sa so da kauna tsakanin ma’aurata.
5. Ki fahimci dabi’ar mijin ki da yanayin shi (kamar
tsanani, saurin fushi, rashin son hayaniya, da makamantan su) saboda ki nisanci
ababen da suke sabanin dabi’ar sa, ko kuma wadanda suke janyo fushinsa ko bacin
ransa.
6. Ki kula da ababen da yake sha’awa kuma yake so,
kuma ki maida hankali wajen kulawa dasu, saboda kowane miji yana da wasu ababe
da yake sha’awa kuma yake so, mace mai wayo tana fahimtar cewa yi masa ababen
da yake so kuma yake sha’awa itace hanya mafi sauki wajen samun kaunar sa da
kuma jin dadin zaman aure da shi.
7. Ki kula sosai wajen sabuntawa da chanji acikin
abubuwan ki, kama daga wajen qawata daki, da jeren ki, da girki (musamman),
saboda tsayawa akan hanya daya kawai yakan kawo qosawa da gajiyar miji har ya
kai baya sha’awar abubuwan da kike yi.
8. Ki guji yawaita qorafi, saboda mafi qyamatuwar
mace a wurin maza itace mace mai yawan korafi, abun ma yakan kara muni idan
qorafin ya kasance a gaban wasu kike yi, kamar makwabta, da danginsa ko naki.
9. Idan
mijinki ya aikata maki abinda bakiji dadin sa ba ko ya bata maki rai, kada ki
yi masa fada ko ki daga sautin ki saman nasa a gaban mutane, ko yaransa, ko
kuma a wajen da akwai mutane ko ake jin sautin ki. Amma ki bari sai kin kebanta
daga ke sai shi, kuma kinga ya sauko (idan fushi yakeyi), kuma kiyi masa Magana
da murya mai taushi, da kalamai masu tasiri, a wannan lokacin zai baki dukkan
hankalinsa ya saurare ki kuma yay i maki abinda kike so, da yawan mata suna
samun matsala da mazajensu saboda sun jahilci wannan hakikar.
10. Idan mijin ki bai yi maki abin da ya kamata
yayi maki ba, ko kuma kina da bukatar wani abu daga gareshi, to gabani ki nema
ki fara gabatar da wasu kalamai wadanda suka kunshi yabo da jinjina da kuma
ambaton halayensa masu kyau, sannan ki ambaci bukatar ki, kashedin ki da inkari
(musun) alkhairin da yayi maki, saboda wannan yana daga cikin Butulcewa abokin
zama (kamar yadda Annabi SAW ya nuna), kuma wannan yana daga cikin abinda ke
bata kauna tsakanin ma’aurata.
11. Ki qawata rayuwar ki ta aure da nuna kauna da
soyayya ga mijinki da zantukan ki kuma aikin ki ya nuna hakan, kada ki sanya
rayuwar ki busassa ta yadda baki nuna masa so ko kauna, saboda rashin nuna masa
so da kauna, da yawaita mashi matsaloli a cikin rayuwar ku ta aure, shine ke
sanya yawancin maza fita waje domin neman wanda zai nuna masu kauna, daga
karshe ya kawo maki abokiyar zama (wadda zata yi mashi wannan).
12. Kada ki cika neman abubuwa daga mijin ki
musamman bukatun da suka shafi KUDI, sannan ki kasance mai lura da yanayin da
miji yake ciki (misali bai amshi albashin wata biyu ba, ko ana damun sa da
kudin haya ko bashi da sauransu), sannan bukatar ki ta kasance cikin lokacin da
ya dace, ba lokacin da yake son ya huta ba ko sadda yake cikin damuwa, sannan
bukatar ta zama wadda babu makawa sai any ice, saboda maza bas a son mace mai
yawan naci da neman bukatu dare da rana.
13. Ki kula da umarnin mijin ki a halin tafiyar sa
da sadda yake gida, sannan kada ki saba masa koda a cikin abubwa masu sauki ne,
sannan kada ki yada sirrin sa, kuma kada ki ambaci nakasun sa da aibinsa ga
kowa ko meye kusancin ki dasu, sannan ki rika ambaton sa da alkhairi a wajen
wasu, (ki tuna da qissar Annabi Ibrahim AS da matan dansa Isma’il AS), yin
hakan zai sanya ya kara aminta da ke, sannan tona masa asiri da aibata shi ba
abinda zai jawo maki illa rashin ganin girman ki da shi mijin zai yi da kuma
wautar da ke da walakanta ki da sauran mata zasuyi.
14. Ki dogara ga Allah sannan kuma ki yarda da
kanki wajen walwale matsalolin gidan ki, kashedin ki da fitar da matsalolin ki
waje, ko kuma gun kawaye, sannan kiyi amfani da duk hanyoyin da suka dace wajen
walwale su, saboda ita matsala idan ta fita ta yadu ta girmama sai shaidan ya
shiga ciki, Allahumma sai in matsalar ta fi karfin ki sai ki nemi shawarar ma’abota
addini da masu hikama wajen walwale ta.
15. Ki cika rayuwar mijin ki da dukkan komai, kuma
ki yi musharaka da shi wajen damuwarsa, da farin cikin sa, kuma ki saba masa da
yin dukkanin abubuwan sa hatta yi masa hidima cikin kananan abubuwa, haka zai
sa idan ya fuskanci wata matsala zai dawo gareki don neman shawara, kuma zai
kasance mai bukatuwa gareki a cikin dukkanin lamuran sa.
16. Kashedin ki da zama WALLAAJAH: wadda take fita
da zarar mijin ta ya fita, fitar ki daga gida ta kasance sai in bukata mai
girma ce ta taso, kuma idan zaki fita ki nemi izini sa, sawa’un yana gari ko
yayi tafiya, saboda yawan fitar mace daga gidan mijin ta yana raunana alaka
tsakanin su, kuma wannan shine ke sanya mace ta rika barin aikata abinda ya
dace tayi cikin gidan ta.
17. Kada ki kasance mai son abin duniya acikin
tasarrufin ki da mu’amalolin ki da mijin ki, sannan idan kika ba mijin ki wasu
kudi ko kika yi masa alkhairi, kada ki yi masa gorin abinda kika yi masa,
saboda wannan zai cutar dashi, kuma idan Allah ya baki abin da zaki yiwa kanki
lalura kada ki takura kice sai yayi maki, kuma ki kasance mai karamci a wajen
kyauta.
18. Ki qawata kanki da kunya da muru’ah acikin mu’amalar
ki da mijin ki, kuma ki kasance mai kyawawan dabi’u, ki nisanci zagi, ki sanya
mijin ki ya ji nauyin ki saboda kirkinki, idan kuma yay i abinda kika kyamata
daga gareshi, ki sanya shi ya fahimci haka daga fuskar ki, saboda wannan uslubi
yana da tasiri sosai.
19. Ki aikata abubuwan da zasu sa mijin ki ya
aminta da ke, kada li yaudare shi, kuma kada ki munana zato gareshi, kada ki
saurari waswasin shaidan da maganganun kawayen ki (munanan kawaye), domin duk
sadda mace ta bada kunnen ta domin sauraren wannan, to kofar sharri babba ce
take budewa kanta, wanda wannan yana iya kiawa ga rabuwa (wal’iyazubillah).
20. Ki kasance mai fadin gaskiya tare da mijin ki a
koda yaushe, a kuma cikin komai, kuma ki sanar dashi duk abinda ke faruwa a
cikin rayuwar ki, kuma idan wata matsala ta faru ki sanar dashi tun farko ba
sai lamari ya ta’azzara ba daga bisani ki sanar da shi, saboda wannan zai iya
kawo mummunan zato da kuma zargin ki akan hakan.
Daga karshe ki kula da duk abinda zai qarfafa alaqa
tsakanin ki da mijin ki, ki nisanci duk abin da zai raunana ta ko ya gusar da
ita. Ina rokon Allah ya albarkaci matan musulmi, a duk inda suke ya kara alakar
so da kauna tsakanin su da mazajen su.
Dan uwanku:
Mustafa Yakubu Lugga
Email: mustafayakubu@gmail.com

Comments
Post a Comment