Posts

Showing posts from December, 2017

KYAKKYAWAN KARSHE DA MUMMUNAN KARSHE

Hakika godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa muna neman taimakon sa da agajinsa muna neman gafarar sa, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabinmu Muhammadu SAW, da iyalan gidan sa masu tsarki, da sahabban sa yardaddun Allah, da duk wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar karshe. Bayan haka ya ku mutane, kuji tsoron Allah madaukakain sarki, sannan ku sani cewa kowane ajali rubutacce ne, sannan kuma wannan rayuwar da kuke cikinta mai karewa ce, Allah SWT yace; “Duk wanda yake kan doron kasa mai karewa ne, fuskar ubanjikinka itace zata wanzu, ma’aboci girma da karamci.” Rahman, 19. “Dukkan wata rayuwa mai dandanar mutuwa ce…..” Aal-Imran, 175. Ita mutuwa lamari ne wanda kowa da kowa ya sallama game da ita, mutane sunyi ijma’i da ittifaki aakn ta babu wani sabani akan mutuwa tsakanin mutane baki daya, muminin su da kafirin su duk zancen su guda ne dangane da mutuwa, ba don komi ba saboda ita mutuwa al’amari ce wadda a koda yaushe...