Posts

Showing posts from 2017

KYAKKYAWAN KARSHE DA MUMMUNAN KARSHE

Hakika godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa muna neman taimakon sa da agajinsa muna neman gafarar sa, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabinmu Muhammadu SAW, da iyalan gidan sa masu tsarki, da sahabban sa yardaddun Allah, da duk wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar karshe. Bayan haka ya ku mutane, kuji tsoron Allah madaukakain sarki, sannan ku sani cewa kowane ajali rubutacce ne, sannan kuma wannan rayuwar da kuke cikinta mai karewa ce, Allah SWT yace; “Duk wanda yake kan doron kasa mai karewa ne, fuskar ubanjikinka itace zata wanzu, ma’aboci girma da karamci.” Rahman, 19. “Dukkan wata rayuwa mai dandanar mutuwa ce…..” Aal-Imran, 175. Ita mutuwa lamari ne wanda kowa da kowa ya sallama game da ita, mutane sunyi ijma’i da ittifaki aakn ta babu wani sabani akan mutuwa tsakanin mutane baki daya, muminin su da kafirin su duk zancen su guda ne dangane da mutuwa, ba don komi ba saboda ita mutuwa al’amari ce wadda a koda yaushe...

YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI!!! SHAWARWARI ASHIRIN (20)

Image
Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai babu abokin tarayya, Tsira da Aminci su tabbata akan wanda babu wani Annabi bayansa, da iyalan gidansa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa rana sakamako. Bayan haka; Wannan wata nasiha ce  da aka gabatar a wajen walimar wata daga cikin ‘yan uwa (Allah ya bata zaman lafiya). Kamar yadda yake, mata na kaunar ace sun mallake zukatan mazajen su, ta yanda kowane lokaci mazajen suna jin dadin zamantakewar su da matan kuma suna kaunar su matuka, ta yanda wannan yakan kai wasu matan zuwa ga halaka ta hanyar neman wannan (mallake mazajensu) inda wasu ke zuwa wajen bokaye da malaman tsibbu. To ‘yar uwa albishirin ki, zaki iya mallake mijin ki ta hanyar da addini ya yarda, wannan hanya itace kyautata mu’amala tsakanin ki da shi, kamar yadda wani mai hikima yake cewa acikin wasu baitoci; Ka kyautatawa mutane zaka mallake zuciyar su, saboda sau da yawa kyautatawa ta kan bautar da mutum (wajen wanda yake kyautata...

FATAWAR LAJINATID-DAA'IMAH: IDAN RANAR IDI TAYI DAI DAI DA RANAR JUMA'AH.

Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai babu abokin tarayya, Tsira da Aminci su tabbata akan wanda babu wani Annabi bayansa, da iyalan gidansa da sahabbansa. Bayan haka; Hakika tambayoyi sun yi yawa akan idan ranar idi ta kasance a ranar juma’a, idi biyu suka hadu; Idul fitr ko Idul adhaa da kuma Idin Juma’a wadda itace idin sati, shin sallar juma’a tana wajaba akan wanda ya halarci sallar idi (fitr ko adhaa)? Ko kuwa sallar idin ta ishe shi sai yayi sallar azahar a maimakon yayi sallar juma’a? sannan shin za a yi kiran salla a wajen sallar azahar a cikin masallatan anguwanni ko kuwa baza a yi ba? Da dai sauran tambayoyi masu alaka da hakan. Sai Lajinatid-Daa’imah ta ga dacewar fitar da fatawowin dake tafe: AMSA: A cikin wannan mas’ala akwai hadisai marfu’ai (hadisin da aka samo daga Annabi ﷺ) da kuma aathaar maukufai (hadisin sahabbai), daga cikin su; 1. Hadisin Zaid bn Arqam (RA) cewa Mu’awiyah bn Abi Sufyan ya tambaye shi: shin ka taba shaidawa a lokacin Annabi ﷺ idi biyu sun ...

KA KOYI LADABIN ILIMI KAMAR YANDA KAKE KOYAN ILIMI.

Image
Assalamu alaikum Magabata na kwarai sun kasance suna fifita ladabin ilimi akan ilimi,suna fara koyan ladabin malamansu kafin su koyi ilimi awajan su,kuma suna koyan ilimi tare da labadi da halaye masu kyau na malaman su,sai hakan ya sanya Allah ya sanyawa ilimin su albarka mai yawa. Wannan shine babban bambanci tsakanin masu ilimi na magabata da masu ilimi na wannan zamani,mafi yawancin masu neman ilimi na yanzu muna neman ilimin ne kadai ba tare da ladabi da tarbiyya ba,zaka sami Dalibin ilimi ga ilimin amma a bangaran ladabi da tarbiyya zero yake kai kace a Tasha ya koyo ilimin,babu girmama ilimin babu girmama malaman da yake koyan ilimin a wajansu,mafi yawansu ma suna barin wajan neman ilimin ne saboda jayayya da malaman su da kuma raina su,sai kaji suna cewa malaman bai iya Nahwu ba baya da balaga da dai sauransu.  *Maganganun magabata na kwarai ladabi* ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺑﻦ ﺣﺒﻴﺐ - ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ; *"Yana yi ma dansa wasiyya sai yake ce masa;Ya kai dana, katafi neman ilimi waj...

MAGANIN MALLAKAR MIJI

Image
Mace ko ta san cewa mallakar namiji haramun ce za ta so a ce ta mallaki nata, na taba jin wata tana neman maganin da za ta mallaki mijinta a wajen mijin yarta. Sai na kasa gane wa zan wa dariya a cikinsu, shi din ba ya gudun in ya ba ta ta ba yayarta? Ko ita ba ta tunanin zai ji tsoron ba ta sabo da haka? Ta dai rantse ta maya kan cewa ba mugun nufi take yi ba, ita kawai tana son ta mallake shi ne don su zauna lafiya, alhali ita kadai ce a wurinsa, gaskiya in ka fahimci wani abu ka yi min bayani, in mace ta karbi ragamar gida ne za a zauna lafiya? Bari na ba ki maganin mallakar namiji mai matuqar aiki, wannan an jarraba shi sam ba shi da side defects duniya da lahira. In kina son ki samu naki maganin koma maganar da uwayenki suka yi miki kafin a kai ki dakin miji ta cewa "Yi na yi, bari na bari" wannan ya ishe ki ki mallaki zuciyarsa. Me yuwuwa ki ga kina shan wahala wajen yi masa duk abin da zai taimaki rayuwarsa amma ba ya gani, qila kin dauki cewa qwaqwalwarki da ...

DALILAI GOMA (10) DA ZAISA MUMINI YA QYAMACI ADDININ SHI'A DA DAN SHI'A.

1. Dan Shi'a yana kallon duk Sahabban Annabi kafirai ne sunyi ridda bayan wafatin Annabi SAW ban da mutun biyar (5). ka diba kuwa a Hajjin bankwana Annabi SAW yayi tare da Sahabbai fiye da dubu 100. 2. Dan Shi'a ya cire matan Annabi da ga cikin iyalan gidan Annabi SAW kuma yana masu kallon kafirci. 3. A addinin Shi'a Qura'nin da kake amfani dashi bai cikaba, yana da nakasu dan an rage wasu surori ko ayoyi a cikin wasu surori. 4. Ba ka shiga Addinin Shi'a sai ka karyata Manzon Allah ta hanyar bada sheda cewa Annabi yayi karya da yace Abubakar, Umar, Usman da sauran Shidda 6 na mutanen da Allah ya basu certificate tun nan duniya ta shiga Aljjanna sai ka karyata Manzon Allah ka tabbatar da yan wuta ne sann an zaka karbi Shi'a. 5. A addinin Shi'a duk wanda ya qudurce ko ya aminta da Khalifancin Sayyidina Abubakar As-Siddiq to kafiri ne kuma jininsa ya halatta. 6. Suna tozarta Al-Qur'ani da Hadisan Annabi da karyatasu ta yadda in Allah yace abu sai su da...