FATAWAR LAJINATID-DAA'IMAH: IDAN RANAR IDI TAYI DAI DAI DA RANAR JUMA'AH.
Godiya ta tabbata ga Allah shi kadai babu abokin tarayya, Tsira da Aminci su tabbata akan wanda babu wani Annabi bayansa, da iyalan gidansa da sahabbansa. Bayan haka; Hakika tambayoyi sun yi yawa akan idan ranar idi ta kasance a ranar juma’a, idi biyu suka hadu; Idul fitr ko Idul adhaa da kuma Idin Juma’a wadda itace idin sati, shin sallar juma’a tana wajaba akan wanda ya halarci sallar idi (fitr ko adhaa)? Ko kuwa sallar idin ta ishe shi sai yayi sallar azahar a maimakon yayi sallar juma’a? sannan shin za a yi kiran salla a wajen sallar azahar a cikin masallatan anguwanni ko kuwa baza a yi ba? Da dai sauran tambayoyi masu alaka da hakan. Sai Lajinatid-Daa’imah ta ga dacewar fitar da fatawowin dake tafe: AMSA: A cikin wannan mas’ala akwai hadisai marfu’ai (hadisin da aka samo daga Annabi ﷺ) da kuma aathaar maukufai (hadisin sahabbai), daga cikin su; 1. Hadisin Zaid bn Arqam (RA) cewa Mu’awiyah bn Abi Sufyan ya tambaye shi: shin ka taba shaidawa a lokacin Annabi ﷺ idi biyu sun ...