KYAKKYAWAN KARSHE DA MUMMUNAN KARSHE
Hakika godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa muna neman taimakon sa da agajinsa muna neman gafarar sa, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabinmu Muhammadu SAW, da iyalan gidan sa masu tsarki, da sahabban sa yardaddun Allah, da duk wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar karshe.
Bayan haka ya ku mutane, kuji tsoron Allah madaukakain sarki, sannan ku sani cewa kowane ajali rubutacce ne, sannan kuma wannan rayuwar da kuke cikinta mai karewa ce, Allah SWT yace;
“Duk wanda yake kan doron kasa mai karewa ne, fuskar ubanjikinka itace zata wanzu, ma’aboci girma da karamci.” Rahman, 19.
“Dukkan wata rayuwa mai dandanar mutuwa ce…..” Aal-Imran, 175.
Ita mutuwa lamari ne wanda kowa da kowa ya sallama game da ita, mutane sunyi ijma’i da ittifaki aakn ta babu wani sabani akan mutuwa tsakanin mutane baki daya, muminin su da kafirin su duk zancen su guda ne dangane da mutuwa, ba don komi ba saboda ita mutuwa al’amari ce wadda a koda yaushe ana ganin ta a aikace yau da kullum. Amma abu mai hadari shine akan me zaka cika yaya zaka mutu yaya zamu hadu da allah yana mai yarda da mu, wannan itace babbar tambaya , wannan kuma shine ke hana salihan bayi bacci (kullum suna cike da tsoro da kuma sauna akan meye mutuwa zata cimmasu).
Allah ya ce “Ya kai mutum! Hakika kai mai aikin wahal da kaine zuwa ga Ubangijin ka, wahala mai tsanani, To kai mai haduwa da shi ne.” InShiqaaq, 6.
To makomar Dan adam (a gobe kiyama) yana kasancewa ne gwargwadon abin da ya cika akan sa, abinda ya kammala rayuwarsa akan ta, abinda ya mutu yana aikatawa. Saboda haka ne ya inganta cikin hadisi daga ma’aiki SAW cewa yace: su ayukka Allah yana hukunci akan su ne da abun da mutum ya mutu yana aikatawa. Acikin wani hadisi na daban Annabi SAW yace lallai mutum zai yi aiki irin aikin yan Aljanna, har sai ya kasance tsakanin shi da Aljanna din babu komi face zira’I daya, kwatsam sai littafin da akayi rubutu game da makomar shi sai ya riga shi sai yayi aiki irin aikin ‘yan wuta sai ya mutu a hakan sai ya shiga wutar, sannan wani mutum zai yi aiki irin aikin yan wuta, har sai ya kasance tsakanin shi da wuta din babu komi face zira’i daya, kwatsam sai littafin da akayi rubutu game da makomar shi sai ya riga shi sai yayi aiki irin aikin ‘yan Aljanna sai ya mutu a hakan sai ya shiga Aljanna. Duka wadannan hadisai suna nuna cewa abinda mutum ya mutu akansa shine abinda Allah zai gina hukumci akan sa.
Saboda haka ne Allah yake bamu labarin Annabin sa Yusuf AS yake cewa bayan yayi masa baiwa da ni'imomi masu yawa, sai Annabi Yusuf yake yin addu'a kamar haka “Ya ubangiji na, lallae ne ka bani daga mulki, kuma ka sanar dani fassarar daga fassarar labaru, Ya mahaliccin sammai da kasa! Kai ne Majibinci na a duniya da lahira, Ka karbi raina ina musulmi, kuma ka riskar dani ga salihai.” Yusuf, 101.
Haka nan Allah ya hakaito muna labarin bayin san na gari mumuinai su ma suna irirn wannan adduar
“Ya ubangijin mu! Lallai ne mu mun ji mai kira yana kira zuwa ga Imani cewa, kuyi Imani da ubangijinku. Sai muka yi Imani. Ya Ubangijin mu! Saboda haka ka gafarta mana zunuban mu, kuma ka kankare miyagun ayukkan mu daga garemu, kuma ka karbi rayukan mu tare da mutanenn kirki.” Aal-Imran, 193.
Haka nan Allah ya hakaito mana labarin masu sihirin nan da suka yi imani da Annabi Musa AS, sannan suka koma zuwa ga uban gijin su Allah lokacin da fir’auna yayi masu barazana zai yi masu azaba mai radadi sbd sunyi imani da musa sai suka ce
:
“Kuma ba ka zargin komai daga gare mu face domin munyi Imani da ayoyin ubangijin mu a lokacin da suka zo mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba mana hakuri a kanmu, kuma ka cika mana muna musulmai.” A’araaf, 126.
Alamomin kyakkyawar cikawa: daga cikin su akwai;
*Mutuwa da Kalmar shahada: kamar yadda ya inganta a cikin hadisi daga Ma’aiki SAW duk wanda Kalmar sa ta karshe yayin rabuwa da duniya ta kasance Kalmar shahada to hakika zai shiga aljanna.
*Mutuwa a farfajiyar filin jahadi domin daukaka Kalmar Allah.
*Mutuwa a ranar Juma’a ko daren Juma’a Annabi SAW yana cewa duk wanda ya mutu a ranar juma’a (a matsayin sa na musulmi) ko a daren juma’a to hakika an amintar da shi (an kare shi) daga fitinar kabari.
*Mutuwa yayin da zufa ke fito ma mutum a goshin sa: Annabi SAW yace haka mumini yake mutuwa (da zufa a goshin sa).
*Mutuwa a halin bautar Allah swt ko wani aiki na gari, misali mutum ya mutu yana karatun Al-Qur’ani mai girma ko mutum ya mutu yana sallah, ko yana dawafi, ko yana a halin harama da hajji ko umrah, ko yana saman hanyar neman ilimi ko ya mutu da azumi a bakin sa, Hadisi ya tabbata daga Dan Masu’ud Allah ya yarda da shi yace: Allah yakan tada mutum ne akan abinda ya mutu a kan sa. Shiyasa lokacin da wani mutum yana cikin aikin hajji ya fado daga saman taguwar say a mutu, Annabi SAW yace a birne shi a haka kada a cire masa ihramin sa domin ranar gobe kiyama zai tashi yana mai talbiyya “labbaikallahumma labaik.”
Alamomin mummunar cikawa: daga cikin su akwai;
*Mutum ya mutu alhali yana mai kashe kansa ko yayi dalilin kashe kansa, Annabi SAW yana cewa duk wanda ya kashe kansa abin nan da yayi amfani da shi wajen kasha kansa da shi Allah zai yi masa azaba ranar gobe kiyama.
*Mutum ya mutu yana mai daukar dukiyar ganima (kafin a raba ta) ko yana mai kwaashe dukiyar gwamnati wadda hakki ne na al’umma, mutum ya mutu a wannan halin to mummunar cikawa ce.
*Mutum ya mutu alhali yana aikata alfasha ta zina ko yana sata.
*Mutum ya mutu yana cikin halin maye (shan giya).
*Mutum ya mutu yana aikata ko wane irin zunubi wanda Allah ya haramta, kamar ya mutu yana sauraren kide kide (misali a cikin mota yayi accident), ko a halin daya kebance daga shi sai macen daba muharramar sa ba, ko a halin yana mai saba ma iyayaensa, ko mace ta mutu tana mai saba wa mijin ta, ko muutum ya mutu yana aikata wasannin da Allah ya haramta, ko yana kallon fina finan da Allah ya haramta. Ko ma makamantan sun a wasu zunubai, Allah ya kiyaye mu.
Muna rokon Allah ya azurta mu da kyakkyawan cikawa ya kuma kare mu daga mummunar cikawa.
Allah ka kyautata karshen mu a cikin dukkanin lamurra, ya Allah ka kiyayaye mu daga walakancin duniya da azabar lahira, Allah kaine mai jibintar lamarin mu a duniya da lahira, kasa mu cika muna musulmai kuma ka hada mu da bayinka salihai. Ameen.
Shaykh Usman Muhammad Sani
Khutubar Juma’a, 3/4/1439H, 23/12/2017CE.
Fassarawa:
Mustafa Yakubu Lugga
mustafayakubu@gmail.com
mustafalugga.blogspot.com.ng
Comments
Post a Comment