Labarin wadda Shan miyagun ƙwayoyi ya tarwatsa mata rayuwa.


Wannan baiwar Allah da abin ya shafa, itace da kanta ta bada wannan labari nata mai cike da sosa zuciya da kuma ban takaici, kamar yadda Ash-Shaykh Muhammad Bn Abdirrahman Al-Arify (Daya daga cikin Malamai masu Da’awah a kasar Saudiyya) yake hakaito mana.
Wannan baiwar Allah take cewa:
“Mahaifi na *Limamin Masallaci* ne, a lokacin da na kammala karatun makarantar sakandire ni da Ɗan uwa na, sai mahaifin mu ya tura mu wani gari domin ci gaba da karatun mu na gaba da sakandire a can, a lokacin ina ‘yar shekara 17 shi kuma Ɗan uwa na shekarar sa 19. Bayan da muka isa garin da mahaifin mu ya tura mu karatu, sai muka kama hayar wani gida a cikin gari (mai dauke da dakuna sashe biyu -2 apartments-) ni da Ɗan uwa na, haka nan dai muka fara karatu muka shafe kusan shekara daya muna karatu, a kullum muna yin Magana da mahaifin mu ta wayar salula, duk lokacin hutu sai mu koma gida in ya kare mu dawo makaranta, muna kula da karatun mu sosai, muna kula da Ibada da kuma sallah akan lokaci. Sannan kudin da suke shigo mana na scholarship suna isar mu, bama neman ko sisi daga mahaifin mu.
“Bayan shuɗewar kusan shekara daya da watanni ‘yan kaɗan, sai Ɗan uwa na ya fada cikin tarkon miyagun abokai, suka sa shi ya fara shan kayan maye, da kaɗan kaɗan kuma suka sanya shi ya fara shan ganye mai bugarwa (wiwi –marijuana-) da dai sauran kayan shaye-shaye har abin ya bi jikin sa.
Take cewa: “Na kasance dani da Ɗan uwa na duka dalibai ne mu da muka kammala makarantar hardar Al-Qur’ani mai girma, kuma ya kasance (a da) yana shafe mafi yawan yinin sa wajen Halƙoƙin hardar Al-Qura’ni a cikin masallaci. Ni kuma na kasance lokacin da na hardace Al-Qur’ani na fara harkar yin Da’awah. A lokacin da na ga Ɗan uwa na ya faɗa cikin wannan mummunan halin, sai na ɗauki matakin yi masa nasiha da kuma tunatar da shi abinda ya riga ya sani, wani lokaci ya tuba daga baya kuma ya koma wa halin sa.
“Wata rana da ya dawo sai ya zo da abin sha (juice) sai yace min ga lemun kwalba nan na zo maki da shi, sai nace masa; ai ko ina son sa, sai na sha wannan lemun. Bayan da na sha wannan lemun sai naji wani yanayi mai ban mamaki, bayan wannan yinin kullum idan zai dawo sai ince dashi ya zo min da irin wannan lemun saman hanyar shi ta dawowa, sai daga baya ne na gane cewa ashe yana jefa kayan maye ne cikin wannan lemun da yake kawo min, sai shedan ya ƙawata min abin, har sai da na wayi gari ina shan kayan maye kamarsa, ina shan wiwi, har saida muka koma muna yiwa kanmu allurar ƙwaya (heroine).
“Kwanaki suka shuɗe, wata rana duka allurar mu ta kwaya ta ƙare illa allura daya wadda take hannun Ɗan uwa na, sai na riƙa yi masa magiya ina sumbatar tafin ƙafar sa ina roƙon sa da ya bani wannan allurar in yi, shi kuma ya ƙeƙashe ƙasa yace bazai bani ba, lokacin da yaga ina kuka sai yace, “ki cire tufafin ki, sannan ki bani dama in aikata alfasha da ke sannan zan baki allurar kiyi”. Sai na cire tufafi na, na bashi dammar aikata zina dani, bayan ya gama abin da yake yi, sai ya jefa min allurar kamar yadda ake jefawa kare ƙashi, nikuma na dauka na soka wa kaina allurar na bugu.
“Wata rana kuma, munje wajen dealer ɗinda yake sayar mana da kayan maye, muka roƙe shi da ya bamu ƙwaya daga baya mu biya shi kuɗinsa, shikuma yaƙi, ya hana mu ƙwayar, bayan har mun juya zamu tafi, ranmu ɓace sai ya cewa Ɗan uwa na, idan na amince masa da kaina zai bamu ƙwayar a kyauta, sai Ɗan uwa na ya tura ni cikin wani ɗaki, daga karshe mutumin ya bamu allurar ƙwaya guda daya sai na raba ta nida Ɗan uwa na. Kwanaki suka yi ta shuɗewa ni da Ɗan uwa na yunwa ta yi mana mugun kamu, domin duk abinda muke samu na scholarship muna amfani dasu ne wajen siyan kayan maye, har ta kai wani lokaci muna zuwa gidajen cin abinci, muna tsintar sauran abincin da mutane suka rage, saboda mu rage raɗaɗin yunwar da ke damun mu.
“Wata rana kuma, daya daga cikin abokan Ɗan uwa na yazo wajen mu, tare dashi akwai wata allurar ƙwaya, nayi ta yi masa magiya ya bani ita, sai ya ƙi bani, yace in mallaka masa kaina zai bani ita, da na ji yace haka sai na riga shi isa cikin ɗaki na cire tufafi na, yace dani in lashe masa takalmin sa da harshe na, sai na lashe masa takalmin sa da harshe kamar yadda kare keyi, har saida takalmin ya jiqe da yawun baki na, sannan kuma ya auka mani, daga baya sai ya jefa min allurar. Sau da yawa abokan sa suna zuwa wajen mu da ƙwaya, su walaƙanta ni su walaƙanta Ɗan uwa na, wani lokaci su sa inyi tsirara a gaban su sannan su bani ƙwaya.
“Wani lokaci kuma sai in kira mahaifin mu, in ce masa muna da jarabawa, muna buƙatar kuɗi mu sayi littafai, sai ya turo mana daga cikin halattacciyar dukiyar sa, amma sai mu sayi ƙwaya da kayan shaye-shaye da su. Shi kuma a zaton sa muna amfani da kuɗin ne wajen karatu. Wasu lokutta idan na shiga ban ɗaki sai jini ya rika zubo min, jini ɓarin cikin shaggun da nayi ne (saboda shaye-shayen da nake yi yana hana cikin zaunawa).
“Haka halin mu ya kasance, har saida wata rana daya daga cikin Ɗaliban da muke karatu tare ta samu lambar wayar gidan mu, ta kira su ta sanar dasu gaskiyar lamarin halin da muke a ciki. Sai Mahaifin mu ya aiko Babban yayan mu domin ya zo ya ganewa idonsa abin da ke faruwa. Lokacin da yazo sai ya isko mu tsirara mun yi shaye-shaye mun bugu bamu cikin hayyacin mu, sai ya dauki ƙyalle ya yafa mini, sannan ya kira motar asibiti aka kaimu Asibitin masu taɓin hankali domin a yi mana magani, a nan ne aka gano cewa mun dade muna shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, kuma muna dauke da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki (HIV AIDS). Aka yi mana magani na wasu watanni, daga baya sai aka sallame mu, Na koma garin mu.
“Yanzu haka ni da Ɗan uwa na muna ɗauke da cutar ƙanjamau (AIDS) , ga kuma zunubban da muka aikatawa ubangijin mu, ga cin amanar da muka yiwa mahaifin mu da kuma zubar masa da mutunci da mukayi. Ni dai kawai ina Roƙon ALLAH mai gafara ya Gafarta mana zunubban mu...
*Wannan kaɗan ne daga cikin illolin da kayan maye da shaye-shaye suke haifarwa cikin wannan al’umma tamu, kuma basu gushe ba suna faruwa akan matasan mu, a cikin garuruwa (a gaban iyaye) da jami’o’i (bayan idanun su).*
Allah SWT yana cewa: “Kada ku kashe kawunan ku, Lallai Allah mai rahama ne a gareku…”
Kuma Allah SWT yana cewa: “Kada ku jefa kawunan ku, da hannayen ku cikin halaka...."
Kuma Allah SWT yana cewa: “...Yana halatta masu daɗaɗan abubuwa, kuma yana haramta masu munanan abubuwa…”
Wannan itace giya, Uwar duka laifuffukan saɓon Allah, wadda ta lalata zukata da yawa, ta mayarda wasu yara marayu, ta gwaurantar da wasu matan, mutane babu iyaka da suka haukace sanadiyyar ta, kuma mutum nawa ne aka kulle a gidan yari saboda ita?, kuma mutum nawa ne aka binne su a makabarta saboda kwankwaɗar ta?.
Wannan itace giya, wiwi, shalisho, cocaine, kwaya….. sunayenta sunyi yawa, illolin ta kuma sun wanzu a bayan ƙasa, tayi tasiri wajen tarwatsa rayuwar samari da yawa, Ya Allah ka ceto samarin mu da suka auka cikin wannnan musibar, ka kiyaye wadanda basu auka mata ba, ya Allah ka ci gaba da kiyaye mana samarin musulunci. Aameeen.
Fassarawa da Rubutawa:
Mustafa Yakubu Lugga
mustafayakubu@gmail.com
www.mustafalugga.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI!!! SHAWARWARI ASHIRIN (20)

KYAKKYAWAN KARSHE DA MUMMUNAN KARSHE

KA KOYI LADABIN ILIMI KAMAR YANDA KAKE KOYAN ILIMI.