MAGANIN MALLAKAR MIJI



Mace ko ta san cewa mallakar namiji haramun ce za ta so a ce ta mallaki nata, na taba jin wata tana neman maganin da za ta mallaki mijinta a wajen mijin yarta.

Sai na kasa gane wa zan wa dariya a cikinsu, shi din ba ya gudun in ya ba ta ta ba yayarta? Ko ita ba ta tunanin zai ji tsoron ba ta sabo da haka?

Ta dai rantse ta maya kan cewa ba mugun nufi take yi ba, ita kawai tana son ta mallake shi ne don su zauna lafiya, alhali ita kadai ce a wurinsa, gaskiya in ka fahimci wani abu ka yi min bayani, in mace ta karbi ragamar gida ne za a zauna lafiya?

Bari na ba ki maganin mallakar namiji mai matuqar aiki, wannan an jarraba shi sam ba shi da side defects duniya da lahira.

In kina son ki samu naki maganin koma maganar da uwayenki suka yi miki kafin a kai ki dakin miji ta cewa "Yi na yi, bari na bari" wannan ya ishe ki ki mallaki zuciyarsa.

Me yuwuwa ki ga kina shan wahala wajen yi masa duk abin da zai taimaki rayuwarsa amma ba ya gani, qila kin dauki cewa qwaqwalwarki da tunaninki sun dara nasa, shi ya sa za ki yi sabanin abin da yake so don jin dadin rayuwarsa.

To bari ki ji, koma baya ki yi tunanin karatun gyatumarki, duk abin da yallaboi baya so tsaya nesa da shi, ko a gabansa ko a bayan idonsa.

Wanda yake so maza aikata, ko ki yi qoqarin aikatawa in kin ka sa ki nuna masa gazawarki kafin shi da kansa ya gano ba ki yi ba, ki yi iya qoqarinki kar a maimaita.

Kar ki yarda ransa yana baci a dalilinki masamman in ba ke kadaice a wurinsa ba, ki tuna duk lokacin da za ki baqanta masa, wata faranta masa za ta yi, tanan kin sami baraka.

Sai kuma kar ki yarda ya fahimci ba ki da amana, ko kin cika son kanki ko naki.

Ga shinan dai kyauta, in kuma kina ganin na mai-gobe-da-nisa ya fi nawa to shi kenan.

Rubutawa:
Baban manar Alkasim
Posting:
Mustafa Yakubu Lugga
mustafayakubu@gmail.com

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YADDA ZAKI MALLAKE MIJIN KI!!! SHAWARWARI ASHIRIN (20)

KYAKKYAWAN KARSHE DA MUMMUNAN KARSHE

KA KOYI LADABIN ILIMI KAMAR YANDA KAKE KOYAN ILIMI.